Mu leƙa Kannywood: Hadiza Gabon ta gasa ma wani bakar magana, karanta abin da ya haɗa su
Fitacciyar yar wasan Hausa, Hadiza Gabon ta mayar ma wani abokinta a shafin Twiter amsa cikin bacin rai yayin da ya bata shawarar lokaci yayi da ya kamata ta fitar da miji.
Jaridar Daily Trust ta Mutumin mai suna M.Bash yana baiwa Hadiza Gabon shawara yayin dayake tsokaci a wani sabon hoto da Hadizan ta daura a twitter, inda yace mata “Masha Allah an girma, ai ya kamata a fidda miji”
KU KARANTA: Da ɗan gari akan ci gari: An kama jami’an hukumar kwastam guda 28 dake da hannu wajen safarar makamai
Jin wannan ya bata ma Hadiza Gabon rai, inda ta amsa da cewa “Toh ko zaka bawa tsoho shawaran ya ma tsohuwa retire ya kawo ni ne?” kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Ga dai yadda takaddamar ta kasance:
M.Bash @muhammadbinbas1 Replying to @AdizatouGabon "Masha Allah an girma ai ya kamata a fidda mijin #AURE"
Hadiza AliyuVerified account @AdizatouGabon Hadiza Aliyu Retweeted M.Bash
"Toh ko zaka bawa tsoho shawaran ya ma tsohuwa retire ya kawo ni ne?"
Sakamakon takaddamar data barke, sai jama’a suka shiga tsakani, inda wani mai sunaSkenxy slux @Auwalmesalati ya amsa da cewa “Pls adinga danne xuciya, i dont think parent has anything to do with this sis, beside aure ba farilla bace sunnah ce, badole bane.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kana iya gayyatar surukan ka biki?
Asali: Legit.ng