Hukumar NNPC ta gano mai a kananan hukumomi 4 na Sokoto

Hukumar NNPC ta gano mai a kananan hukumomi 4 na Sokoto

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya ce aiki ya yi nisa a yunkurin nemowa da kuma hako man fetur da iskar gas a jihar Sakkwato da ke arewacin kasar.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar da ma na jihohi musamman na arewa ke kukan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da karancin kudaden shiga.

Hukumar NNPC ta gano mai a kananan hukumomi 4 na Sokoto
Hukumar NNPC ta gano mai a kananan hukumomi 4 na Sokoto

KU KARANTA: Zaben 2019 ba zai yiwuba inji wani Fasto

Legit.ng dai ta samu cewa ankunan da aka fara gano man a cikin jihar Sakkwato sun hada da Gada da Goronyo da Illela da Gudu da kuma Tangaza.

Wannan bayanin ya fito fili ne bayan ganawar da gwamnan jihar ta Sakkwato ya yi da shugaban kamafanin na NNPC a Abuja babban birnin kasar.

A wani labarin kuma dai mun samu cewa mashahurin dan kasuwar nan kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote watau Alhaji Aliku Dangote yayi kira ga al'ummar kasar nan da su dukufa wajen yin addu'a Allah ya kara karairaye darajar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Babban dankasuwar wanda kuma dan asalin jihar Kano ne ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da yayi da yan kasuwa a lokacin da shugabannin kasashen duniya ke taron su a majalisar dinkin duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng