Matsafa sun sagale Mage a jikin bishiyar kuka a cikin maƙabarta, kalli yadda suka yi ma magen
Ke duniya, ina zaki damu ne? a koda yaushe ana jan hankalin mutane da su fawwala ma Ubangiji Allah dukkanin sha’aninsu, sa’annan su daidaitu akan hanya madaidaiciya, amma ina, wasu basa ji.
Waus sun gwammace su dinga bin bokaye da Malaman tsubbu suna basu umarni marasa kan gado, duk don su cika burinsu na Duniya, lahira kuma ko oho!
KU KARANTA: Haƙar arzikin man fetur: Akalar gwamnatin tarayya ya koma jihar Sakkwato
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani, Facebook, Bashir El-Bash ya bada labarin wani surkullen tsafi da aka gani a wata katafariyar makabarta dake garin Sumaila ta jihar Kano.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamarin daya auku a makabartar, inda aka tsinci wata Mage da aka daure ta cikin wata bakar leda, sa’annan kuma aka sagaleta a jikin wata katuwar bishiyar kuka dake cikin makabartar.
Sai dai jama’an da suka ga wannan bala’i sun ruga wajen Dagacin garin, inda suka kai mai bayani, shi kuma ya gayyaci jami’an Yansanda da su garzaya makabartar don gane ma idanunsu, da isarsu wajen kuwa suka hangi bakar leda, da wani abu yana mutsu mutsu a cikinsa.
Kwancewa ledar ke da wuya, sai ga wata katuwar Mage ta fado tim! daga cikinsa, da aka cigaba da bincika ledar, sai aka gano wasu kayayyakin siddabaru a ciki, wanda ake tunanin kayayyakin tsafi ne.
Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng