Wata 'Yar a Najeriya tayi zarra a gasar jarida ta Duniya

Wata 'Yar a Najeriya tayi zarra a gasar jarida ta Duniya

- Wata daga Arewacin Najeriya ta lashe kyautar gidan Jaridar BBC

- Amina Yuguda 'Yar jarida ce a Arewa maso Yammacin kasar

- Yuguda za ta samu damar yin aiki da gidan Jaridar BBC

Wata baiwa Allah mai suna Amina ta lashe kyautar Komla Dumor na BBC. An kirkiro wannan kyauta ne dai domin tunawa da Komla Dumor a Duniya wanda ya mutu yana shekara 41 a Duniya a shekarar 2014.

Wata 'Yar a Najeriya tayi zarra a gasar jarida ta Duniya
'Yar Najeriya Amina Yuguda ta ci kyautar BBC

Wannan karo wata daga Kasar Najeriya ce ta ciri tuta inda ta lashe kyautar Komla Dumor na gidan yada labaran nan na BBC a wannan shekarar. Amina Yuguda wata 'yar jarida da ta fito daga Yola a Arewa maso Yammacin kasar ce ta samu wannan lambar yabo.

KU KARANTA: Kwastam ta kuma yi wani babban kamu

A halin yanzu Amina Yuguda za ta samu damar aiki da Gidan yada labarai na BBC na watanni uku bayan irin rawar da ta taka a Kasar daga ciki har da dauko rahoton 'yan ta'addan Boko Haram. Yuguda ta nuna matukar farin cikin ta na samun lashe wannan kyauta.

Wata 'Yar kasar Ugunda Nancy Kucingira da Didi Akinyeluresu daga Najeriya su na cikin wadanda su ka taba lashe wannan babban kyautar a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojojin sun zagaye Jihar Abia ana neman Kanu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng