Matsalolin rayuwa sun sanya wani mutum halaka a Kano bayan ya caka ma kansa wuƙa, ya afka rijiya

Matsalolin rayuwa sun sanya wani mutum halaka a Kano bayan ya caka ma kansa wuƙa, ya afka rijiya

Wani mutumi mai suna Balarabe Adamu ya caka ma kansa wuka, sa’annan ya tunjuma cikin rijiya a jihar Kano sakamakon wani abu daya dame shi a ransa.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito Balarabe mai shekaru 40 ya aikata ma kansa wannan aika aikan ne a ranar Talata 19 ga watan Satumba, a unguwar Rijiyar Zaki an jihar Kano.

KU KARANTA: Gwamnati tarayya zata fara aikin manyan hanyoyi 41 a faɗin ƙasar nan

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar bada kashe gobara ta jihar Kano Mustafa Rilwan yana fadin cewa sun samu nasarar ceto Balarabe daga cikin rijiyar, sai dai ya rasu a Asibitin Murtala na jihar.

Matsalolin rayuwa sun sanya wani mutum halaka a Kano bayan ya caka ma kansa wuƙa, ya afka rijiya
Rijiya

Mustafa yace sun samu rahoton abin da Balarabe ya aikata ma kansa ne ta bakin makwabtansa da suka kawo kara.

“Bayan samun bayanan, sai muka garzaya gidansa da misalin karfe 5 na yamma, inda muka ceto shi” Inji shi.

Daga karshe Mustafa ya bukaci jama’a da su dinga fawwala ma Ubangiji Allah komai dangane da matsalolin rayuwa, kuma inda suka nuna yakini sai Allah ya kawar musu da bakin cikinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: