Shugaba Buhari ya godewa sarki Abdalla na Jordan kan gudummawarsa ta kayan yaki don kashe 'yan Boko Haram

Shugaba Buhari ya godewa sarki Abdalla na Jordan kan gudummawarsa ta kayan yaki don kashe 'yan Boko Haram

- Kasar Jordan (Urdan da Larabci), tana gaba-gaba wajen ragargazar mayakan daular Islama ta ISIS

- Sarkin Kasar Jordan yana daga cikin ahlul bayti masu tsatso daga annabi Muhammadu

- Shugaba Buhari ya godewa Sarkin Jordan da irin yawan makaman da yake aikowa Najeriya

Garba Shehu, Hadimi ga shugaba Buhari, ya saki sanarwa a shafinsa na facebook cewa, shugaba Buhari, yayi godiya ga sarki Abdalla na kasar Urdaan, da irin gudummawar da ya baiwa Najeriya domin ragargazar mayakan IS.

Shugaba Buhari ya godewa sarki Abdalla na Jordan kan gudummawarsa ta kayan yaki don kashe 'yan Boko Haram
Shugaba Buhari ya godewa sarki Abdalla na Jordan kan gudummawarsa ta kayan yaki don kashe 'yan Boko Haram

Salon yakin ISIL a cab gabas ta tsakiya, ya chanja ne musamman bayan da kungiyar ta kona wani sojan kasar ta Jordan a keji da ransa, bayan sun harbo jirginsa da yake shawagi a sama.

Sarkin Jordan din da kansa ma ya hau jirgi ya je yayi ma mayakan ISIL ruwan bama-bamai, sai kuma gashi yanzu ya aiko da kayan yaki domin Najeriya ta kakkabe irin nata miiyagun.

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar, ta bada bayanai kan yawan makaman da kasar ta Jordan ta bawa Najeriya, sannan da ma alkawarin jiragen shelikwapta da sauran kayan yaki.

DUBA WANNAN: MAta masu aiki soja sun rasa miji, dubi labarinsu

Ganawar shugaba Buharin dai da Sarki Abdallah, tana zuwa ne a lokacin da ake babban taron majalisar dinkin duniya a birnin New York ta Amurka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng