Ba mu saba da barnar kudi ba-Attajirin Duniya Dangote
- Aliko Dangote ya bayyana cewa shi ba mutum bane mai facaka
- Babban Dan kasuwar yace an fi morar kudin a kan karon kan sa
- Duk Afrika dai babu wanda ya kama kafar Dangote a dukiya
Kwanakin baya idan ba ku manta ba Aliko Dangote yayi hira da Jaridar Bloomberg ta Turai ya kuma bayyana irin tsarin rayuwar sa da kasuwancin sa.
Kasurgumin Dan kasuwar nan na Afrika Aliko Dangote yace shi fa ba mutum bane mai facaka da kudi ko da yana cikin masu kudin Duniya. Dangote yace ko yayi tafiya zuwa kasashen Duniya a dakin otel yake sauka don bai da gida in ba a Najeriya ba.
KU KARANTA: Za a daure wani barawo saboda ya saci siminti
Aliko Dangote a hirar da yayi da Bloomberg TV yace ya fi ganewa neman kudi a kan yayi facaka da su. Dangote yace shi mutum ne mai saukin kai wanda har ta kai shi kadai za ka gani yana tuka mota a kan titin Legas inda yana gida.
Dangote ya kuma cewa idan yana gari musamman a karshen mako gidan sa a bude yake kuma ya kan kai ziyara wajen abokan sa da ya taso tare da su. Dangote yace shi da iyalan sa dai ba su saba da kashe kudin hauka ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko za ka iya gayyatar tsohuwar Budurwar ka zuwa wajen daurin auren ka?
Asali: Legit.ng