An kama motar Dangote makare da daskararrun kaji na miliyoyin naira
Hukumar kwastam ta yi ram da wata motar kamfanin siminti na Dangote makare da kimanin katan 3000 na daskararrun naman kaji wanda farashin su zai kai naira miliyan 47 a jihar Ogun.
Kwamftrollan hukumar sashin jihar Ogun, Sani Magudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba.
A cewarsa bincike da suka gudanar ya nuna cewa kajin sun shigo kasar ne daga kasar Benin.
Inda ya kara da cewa sun samu labarin cewa ‘yan fasa kwauri na amfani da motocin kamfanin Dangote wajen shigo da haramtattun namomin, wanda haka ne ya sa suka dana masu tarko.
Ya ce sun fara bin motar mai lambar rajista ICT-13E-047 tun a gurin da ake kunshe kajin, kafin a yi lodin su kan motar, har sai da suka samu nasarar kama ta akan titin Sagamu zuwa Abeokuta a ranar 16 ga watan Satumba da misalin karfe 3:45 na asuba.
KU KARANTA KUMA: Jawabin shugaba Buhari a taron UN na bogi na yawo – Fadar shugaban kasa
Ya ce samu nasarar damke yaron motan, amma direban tuni ya cikawa wandon shi iska. Ya yi alkawarin cewa za su kama wannan direba tare da duk wadanda ke da hannu a al’amarin.
A lokacin da sanarwar ta fita, kwamfrollan ya ce tuni suka fara binne wadannan namomin kaji.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng