An kama mai shekaru 43 da yin luwadi da yara biyu

An kama mai shekaru 43 da yin luwadi da yara biyu

- Mai laifin Ibrahim ya yaudari yaran da N200 kafin ya kwanta da su

- Rudunar yansandar Jihar Katsina sun fara bincike akan al'amarin

- An taba kama mai Ibrahim da aikata irin wannan laifi a baya

Rundunar yan sandar jihar Katsina sun kama wani Ibrahim mai shekaru 43 da yaudarar wasu yara maza biyu yan shekaru 15 da N200 dan yin luwadi da su.

Mai Magana da yawun hukumar yansandar jihar, DSP Gambo Isaha lokacin da yake tabbatar da aukuwan al’amarin ya bayyana ma yan jarida cewa mai laifin Ibrahim ya yaudare su ne ta hanyar samu musu finafinan batsa na 'Blue fim' kafin ya sadu da su, kuma yace an taba kama shi da irin wannan laifin a baya.

An kama mai laifin ne bayan mahaifin daya daga cikin yaran da ya sadu da su ya kai ma hukumar yansadar Central Police Station kara bayan yaron ya fada ma mahaifiyar abun da aka masa.

An kama mai shekaru 43 da yin luwadi da yara biyu
An kama mai shekaru 43 da yin luwadi da yara biyu

DSP Isah yace an fara bincike game da al’amarin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kamala bincike.

KU KARANTA : Biyafara: Cif wif na majalissar wakilai ya soki Saraki akan al’amarin Nnamdi Kanu, da IPOB

"An taba kama Ibrahim da aikata irin wannan laifi a baya. Mahaifiyar daya daga cikin yaran da aka yiwa luwadi ta fada mahaifin yaron bayan yaron ya fada mata abun da aka mi shi.

“Shi kuma mahaifin ya kai kara ofishin yansada dake Central Police Station. inji DSP za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kamala bincike,” inji DSP Isah.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: