Ko ba jima ko ba dade za a ga amfanin aikin Gwamnatin Buhari Inji mai magana da bakin sa

Ko ba jima ko ba dade za a ga amfanin aikin Gwamnatin Buhari Inji mai magana da bakin sa

- Wani mai taimakawa Buhari yace za a ga amfanun aikin wannan Gwamnatin

- Bashir Ahmad yace makudan kudin da Hukumar EFCC ta samu na nan a ajiye

- Hadimin Shugaban kasar yace ba a nuna bambanci wajen yakar sata a Kasar

A wata hira da yayi da Legit.ng, Bashir Ahmad ya bayyana cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a Gwamnatin Shugaban kasa Buhari.

Ko ba jima ko ba dade za a ga amfanin aikin Gwamnatin Buhari Inji mai magana da bakin sa
Bashir Ahmad yace za a ga aikin Gwamnatin Buhari

Hadimin Shugaban kasar yace an ga aiki da cikawa wajen alkawuran da Shugaban kasa Buhari ya dauka. Malam Bashir yace Shugaba Buhari ya kama yaki da sata a Kasar kuma ba tare da nuna bambancin siyasa ba wanda har wani tsari Gwamnati ta kawo tona asiri-ka samu rabon ka domin yaki da barna da dukiyar Jama'a.

KU KARANTA: Hadimin Buhari yace babu wanda ya isa ya raba kasar nan

Mai taimakawa Shugaban kasar yace kowa ya san irin nasarar da Hukumar EFCC ta samu wajen karbe kudi saga hannun barayin kasar. Ganin dai har yanzu 'Yan Najeriya ba su fara cin romon abin ba yace da zarar Kotu ta bada dama za a gani kasa. Bashir Ahmad yace ko Shugaba Buhari na mulki ko ba ya nan za a amfana don dukiyar Gwamnati ce.

A karshe Hadimin Shugaban kasar yace idan so samu ne ace Shugaba Buhari ya karbe duk kudin da aka sace tun daga samun 'yancin kai kawo yanzu. Ya kuma ce Gwamnati ta na da fika-fiki daga Majalisun Tarayya zuwa Kotun kasa don haka ba zai yiwu Gwamnatin Tarayya kadai ta dauki mataki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojojin Najeriya sun yi Nnamdi Kanu zobe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng