Matashiya yar Igbo, Chinelo Goodluck Nworah, ta bayyana abunda ya wakana tsakaninta da wasu Hausawa biyu (hoto)

Matashiya yar Igbo, Chinelo Goodluck Nworah, ta bayyana abunda ya wakana tsakaninta da wasu Hausawa biyu (hoto)

Duk da banbancin al’ada, wata kyakyawar matashiya yar kabilar Igbo ta je shafinta na zumunta don bayyana yadda ya wakana tsakaninta da wasu Hausawa biyu da suka je gidanta don gyara mata takalmanta.

Matashiyar da aka ambata da suna Chinelo Goodluck Nworah ta bayyana yadda ta ciyar da Hausawan dake fama da yunwa bayan ta basu kudin aikin da suka yi mata.

Nworah ta kara da cewa yan Najeriya yan Najeriya da kansu ne zasu kawo canjin da suke bukata ba wait a hanyar jiran gwamnati ta jagorance su kan haka ba.

Matashiya yar Igbo, Chinelo Goodluck Nworah, ta bayyana abunda ya wakana tsakaninta da wasu Hausawa biyu (hoto)
Matashiya yar Igbo, Chinelo Goodluck Nworah, ta bayyana abunda ya wakana tsakaninta da wasu Hausawa biyu (hoto)

KU KARANTA KUMA: Nnamdi Kanu na shirin tserewa Kamaru – Kungiyar matasan Arewa

Matashiya tace: “Yan mintuna kadan da suka shige, wani bahaushe (mai gyaran takalmi) ya shige ta gida na sai na kira shi domin ya gyara mun takalmi na, yace N50 sai nace toh. Bayan yan wasu mintuna yace ya kammala (sai na tarar dashi tare da wani mai gyaran takalmi a lokacin da na fito). Na bashi N100 ya bani chanjin N50..Sai yace na bashi sauran naira hamsin din don ya siya abinci yaci, cewa shi dad an uwansa basu ci abinci ba. Sai nace masa idan da gaske suna jin yunwa, zan basu taliya da na dafa sai suka nuna farin ciki da hakan. Zancen gaskiya naji dadin yadda na sanya wasu farin ciki ba tare da la’akari da cewan Hausawa ne bay an Biyafara ba. Najeriya day ace ba tare da la’akari da abunda ke faruwa a kasar ba... zaman lafiyar kasar nan zai fara ne daga dukkaninmu.. Ya fara ne daga ni da ku!!”

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng