Dan Arewan da ya ba da mamaki a lokacin bikin yaye daliban makarantar sojoji
- Osinbanjo ya halarci bikin yaye daliban makarantar sojoji a Kaduna
- Ahmed Bature shine dalibin da yafi kowa kokari a wannan shekera
- A tarihin NDA ba'a taba samun dan Arewan da ya samu lambar yabon da Ahmed ya samu
A ranar Asabar 16 ga watan Satumba aka yi bikin yaye daliban makarantar sojoji na NDA Kaduna wanda mataimakin shugaban kasa Ferfesa Yemi Osinbajo ya halarci taron a madadin shugaban kasa.
Wani matashi dan Arewa mai suna Ahmad Bature daga jihar Sokoto ya ba kowa mamaki inda ya lashe dukan wani kyauta a lokacin bikin.
Mutane sun ta tofa albarkacin bakin aka nasarar da Ahmad ya samu a shafikan sa da zumunta. Ahmed Ibrahim Gamawa ya rubuta a shafin sa na Facebook da cewa
"Kuyi hakuri kada kuce na da me ku da labarin nasarorin da wannan mastashi ya sa mu. Dalili shine, yayi abun mamaki wanda yasa kowa ya san shi a lokacin bikin yaye daliban makarantar sojoji na NDA."
KU KARANTA : APC ta amince da Buhari, El-Rufai a zaben 2019
Wannan matashi ya lashe duk wata kyauata a ranar bikin; wanda ya kunshi
1. Takobin girma
2. Garkuwan Indiya
3. Dalibi mafi kokari a wannan shekara
"Babu dan Arewa da ya taba samun irin wannan kyauta a tarihin NDA. Muna alfahari da Ahmed tare da ta ya shi murna".
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng