Kasar Singapore ta samu shugabar kasa mace a karon farko
- Kasar Singapore ta samu shugabar kasa mace a karon farko
- Halima Yacob, ta kasance tsohuwar kakakin majalisa a kasar Singapore kafin zamowarta shugabar kasa
- Ita kadai ce tayi nasarar cika sharudan zama shugabar kasa kamar yadda dokokin kasar ta shimfida cikin yan takaran guda uku
Rahotanni sun kawo cewa kasar Singapore ta samu shugabar kasa mace karo na farko bayan an kaddamar da zabe a kasar.
Halima Yacob, wacce ta kasance tsohuwar kakakin majalisa a kasar Singapore, ta zama shugabar kasa mace ta farko da aka taba samu a kasar.
A cikin ‘yan takaran shugabancin kasar guda uku da suka hada da Salleh Marican da Farid Khan, Yacob ita kadai ce tayi nasarar cika sharudan zama shugabar kasa kamar yadda dokokin kasar ta shimfida, wanda ya gindaya cewa duk dan takara sai ya taba shugabantar kamfani mai zaman kanta wanda hannun jarin sa ya kai dalar Singapore miliyan 500 (kimanin dalar Amurka miliyan 372).
Yacob mai shekaru 63 dai ita ce shugabar kasa mace ta farko a kasar, kuma ‘yar kabilar Malay ta farko a cikin shekaru 47 da za ta zama shugaba.
KU KARANTA KUMA: Hadin kan Najeriya yin Allah ne – Sultan na Sokoto ga masu rikici
A jawabin da ta yi a hukumar zabe ta kasar, Yacob ta jadaddawa mutanen kasar cewa za ta kasance shugabar kasa ta kowa da kowa ba tare da la’akari da banbancin kabila, launin fata ko addini ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng