Daliban sakandari kunnenku nawa? An sako sakamakon jarabawar NECO
- Hukumar shirya jarabawar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar
- An fitar da sakamakon ne a ranar ALhamis 14 ga watan Satumba
Hukumar shirya jarabawar NECO ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar wanda aka zana a watannin Yuni da Yuli na shekarar 2017, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban hukumar NECO, Farfesa Charles Uwakwe ya sanar da fitar da sakamakon a ranar Alhamis 14 ga watan Satumba, inda yace dalibai 1,055,988 ne suka zana jarabawar.
KU KARANTA: Gwamnatin Indonesiya ta aika ma Musulman Rohingya tallafi, yayin da aka yi zanga zangar nuna ɓacin rai a Indiya
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wandada suka zana jarabawar su 745,053 ne suka samu sakamakon mai kyau, inda suka samu maki mai darajan ‘C’ a darussa 5 da suka hada da harshen Ingilishi da lissafi.
Farfesa yace dalibai 903,690 ne suka samu sakamako mai kyau a darasin yaren Turanci, yayin da 849,335 suka samu darajar C a lissafi. Bugu da kari an samu masu satar amsa su 50,586, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Akwai makarantu 276 da aka kama su da satar amsa a jihohi 34, yayin da aka cire makarantu 6 daga jerin wadanda zasu dinga gudanar da jarabawar, haka zalika an kama jami’an hukumar su 23 da laifin taimaka ma masu satar amsa. Ana iya duba sakamakon jarabawar a https://www.mynecoexams.com
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng