Yaga uwar bari: Mata ta matsafiya ce, tana ɓacewa a duk lokacin data ga dama, a raba mu – Inji Miji ga Alkali
Wani mutum dan jihar Legas, Olarenwaju Moruf ya bayyana ma alkalin kotun gargajiya dake Igando cewa matarsa matsafiya ce, don har tana bacewa tana dawowa, inda ya bukaci a raba auren nasu.
An yi wannan shari’a ne a ranar Alhaimis 14 ga watan Satumba, a gaban alkali Adegboyega Omilola, inda Moruf ya shaida ma Kotu cewa bawa bukata cigaba da zama da matarsa Fatima, wanda suka kwashe shekaru 17 a tare.
KU KARANTA: An gurfanar da fastoci 2 a kotu bisa zargin sace yarinya mai shekaru 2
“Akwai ranar da mata ta ta bace tun daga jhar Legas, sai na ganta a Arewa a dakin Otel dina lokacin da naje neman aiki, a lokacin da nayi ihu sai ta bace. Matar nan na zuwa min a duk lokacin da wani abin alheri ya same ni.
“Duk inda naje neman magani, sai a tabbatar min cewa mata tace matsalar rayuwata, a takaice dai matsafiya ce.” Inji Moruf.
Moruf yace ya taba kama matarsa ta shirya taron matsafa a gidansu, cikinsu har da wani karamin yaro, wanda an san mahaifin, gawurtaccen matsafi ne.
Sai dai a nata bangaren, Fatima ta musanta zarge zargen, inda tace ita fa ba matsafiya bace, “Bani da hannu cikin matsalolin mijina, ni musulman kwarai ce.” Inji ta, sa’annan ta roki kotu da kada ta kashe auren.
Daga karshe sai alkali Adegboyega ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba don cigaba da sauraron karar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng