Neman maganin ciwon kai yasa an damfari wani dan kasuwa miliyan N25

Neman maganin ciwon kai yasa an damfari wani dan kasuwa miliyan N25

- Isiaka ya rasa duka dukiyoyin sa ta sanadiyar neman magani

- Yan damafaran sunyi barazanar kashe Isiaka idan ya tona mu su asiri

- Yansandar Division 2 na jihar Legas sun kama mutane 5 daga cikin masu laifin

A kokarin neman maganin ciwon kai, wani dan kasuwa dake Sango Ota, a Jihar Ogun mai suna Oladimije Isiaka yayi asarar kudi miliyan N25 a hanun yan damfara.

Jaridan Punch ta bayyana cewa dan kasuwan ya sayar da gidan sa da motocin biyar dan samun kudin magani. A lokacin da ya gane an damfare shi, sai ya kai kara zuwa hukumar yansanda dake Zone 2 Onikan, jihar Legas. Wannan yayi sanadiyar kama mutane biyar a cikin wadanda suka damfare shi.

Hukuamar yansadar zone 2 sun bayyana sunayen wadanda ake zargi da laifin, wanda ya kunshi Akeem Alabi, Yetunde Mustapha, Alasela Ottun, Ibrahim Jimoh da Oyegbila Lateef.

Neman maganin ciwon kai yasa an damfari wani dan kasu miliyan N25
Neman maganin ciwon kai yasa an damfari wani dan kasu miliyan N25

Wani majiya ya bayyana wa yansada cewa “Isiaka sirikin Ottun ne kuma ya nemi shawara sa game da ciwon kan sa a watan Oktoba 2016, saboda ya kasa samun magani."

KU KARANTA : Yanzu-yanzu : An kashe Manjo Janar Ugbo da mutane bakwai a rikicin da ya barke a Benuwe

“Isiaka dan harkan mai ne, a lokacin da ciwon sa ya fara, ya nemi taimakon sirikin sa Ottun. Sirrikin ya kiraYetunde Mustapha ta yi mishi adu’a. Ita kuma ta fada ma saurayin ta akan rashin lafiyan Isiaka daganan sai suka fara tamabayan su kudin magani, kuma suka ce 'Jifa' aka yima sa. Daga karshe sun ansa milyan N25 a hanun su."

Mutumin ya sayar da duka dukiyoyin shi, wanda ya kunshi gida da motioci biyar. Yanzu ya daina kasuwanci saboda rashi kudi. Lokacin da suka ga ya fahimci sun damfare shi, sai su ka fara mishi barzanar kashe shi idan ya fada ma kowa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng