Wasu hotunan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi a zamanin rayuwarsa
A ranar 11 ga watan Satumba ne shehin Malami, marigayi Malam Abubakar Mahmud Gumi ya cika shekaru 25 da rasuwa, inda ya rasu a shekarar 1992 a birnin Landan.
Malam Abubakar ya shahara sosai a fagen da’awa, tsantsani da kuma iya mulki a dukkanin mukaman daya rike a zamanin rayuwarsa, inda yayi zama a garin Maru, Kano da Kaduna.
KU KARANTA: An yi ma wani dattijon biri mai yi ma ƙananan mata fyade bulala 25, kalli bidiyon
Malam ya shahara a fannin ilimin Qur’ani, Fiqihu, Hadisi, Tauhidi da kuma ilimin harshen larabci, wanda hakan ya kais hi ga samun lambar yabo na sarkin Makkah sakamakon gudunmuwar dayake baiwa Musulunci.
A zamaninsa Malam ya rike mukamai daban daban, tun daga Malamin makarantar sakandari, zuwa alkalin alkalai na kotun shari’a Musulunci na yankin Arewa 1962–1967, inda ya zamo daya daga cikin manyan mashawartan Firimiyar Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna.
Wasu daga cikin manyan abokanan su sun hada da Aminu Kano, Ibrahim Dasuki, Waziri Junaidu, Shehu Shagari, sa’annan ya baiwa kungiyar Izala gudunmuwa sosai ta hanyar shawarwari, sai dai ba shi ya kafata ba, kamar yadda ya bayyana da kansa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng