Wani jami'in yan sanda ya shiga musabakar Al-qur'ani mai girma a Katsina
Wani labari mai dadin ji da muka samu yanzu ba da dadewa na nuni da cewa wani jami'in rundunar yan sandan Najeriya mai suna Malam Bashir daga garin Funtua ta jihar Katsina ya shiga musabakar gasar karatun Al-qur'ani mai girma.
Kamar dai yadda muka samu daga wani ma'abocin manhajar nan ta Fazbuk mai suna Husain Kyar'adua ya bayyana a cikin wani gajeren rubutu da yayi a shafin sa ya bayyana cewa wannan dan sandan ya fito ne daga karamar hukumar Funtua.
KU KARANTA: Buhari ya fara bincikar Sojin Najeriya
Legit.ng haka ma dai ta samu cewa dan sandan ya shiga musabakar gasar ne a bangaren Hizib 60 da kuma tajwid.
Shi dai Husain Kyar'adua ya rubuta a shafin nasa cewa: "Kamar yadda kuka gani (a nan) Mal Bashir ya gabatar da karatun sa a yau din nan a garin Funtua inda ya shiga Musabakar a matakin Hizib 60 da Tajwid."
"Ko wane irin fata zaku yi masa"? Husain Kyar'adua yayi tamabaya daga karshe.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng