Toh fah! Hotunan fosta na kiranye ga Bukola Saraki sun mamaye garin Ilorin

Toh fah! Hotunan fosta na kiranye ga Bukola Saraki sun mamaye garin Ilorin

- Wata kungiya da tayi wa kanta lakabi da 'Kwara must change' ta watsa fostoci a ilorin tana bukatar Bukola Saraki ya dawo gida

- Kungiyar tayi zargin cewa Sarakin yana wakiltan kansa ne da iyalansa kawai

- Kungiyar har ila yau tace Saraki da mukarabansa suna sayar da guraban aikin al'ummar kwara ta tsakiya

Bisa ga dukkan alamu kakakin majalisan dattawa na kasa Sanata Bukola ya shiga tsaka mai wuya yan kwanakin nan domin a halin yanzu, fostoci da ke dauke da sakon kiranye gareshi duk sun mamaye babban birnin jihar Kwara.

Fostocin duna dauke da sunan wata kungiya da tayi wan kanta lakabi da 'Kwara must change' ma'ana dole jihar kwara ta canja, an mana fostocin a manyan tituna da kananan hanyoyi a jihar.

Toh fah! Hotunan posta na kiranye ga Bukola Saraki sun mamaye garin Kwara
Toh fah! Hotunan posta na kiranye ga Bukola Saraki sun mamaye garin Kwara

Fostan na dauke da sako kamar haka: ''Kwara bata samun wakilci a majalisan dattawa, Sanatan mu kawai kansa yake wakilta.

DUBA WANNAN: Hukumar Hisbah ta kama almajirai 1,429 a Kano

''Saraki da mukarabansa suna sayar da guraben aikin da ya kamata a baiwa 'yan kwara ta tsakiya da ilorin akan kudi har misalin naira miliyan 10. Saraki ya aikata abubuwa da dama wanda basu da amfani ga mutanen kwara da kasa baki daya.

"Mun gaji da yaudarar da yake man, Mu yan ilorin mun gaji haka. Dole mu kawo canji yanzu.''

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164