Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara (hotuna)

Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara (hotuna)

- Wani mutumin jihar Kebbi ya zamo madubin dubawa ga mutane da dama

- Yana tafiyar da rayuwar sa ta hanyar gasa masara da kuma siyar da wasu albarkatun gonar sa

Wani dan Najeriya mai suna Basiru ya zamo abun magana a gari bayan mutane sun gano abunda yake domin tsafiyar da rayuwarsa da kuma yadda yake gasa masara saboda daukar nauyin al’amuran san a yau da kullun.

An wallafa labarin matashin mai ban mamaki a shafin Facebook. A nan, Basiru wanda ya fito daga jihar Kebbi yayi magana game da abubuwan da yake yi don dauke ma kansa matsalolin yau da kullun.

A matsayinsa na manomi, yana siyar da mafi yawan albarkatun gonarsa ga mutane. Idan lokaci yayi na girbe masara, yakan yi hakan sannan kuma ya gasa wasu daga ciki.

Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara (hotuna)
Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara

KU KARANTA KUMA: Suna so mu zama yan ta’adda – Nnamdi Kanu

Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara (hotuna)
Kalli dan Najeriya mai sana’ar gasa masara

Duk da cewar yana fuskantar kalubale daga mutane da dama wadanda ke karyar masa da gwiwa domin a tunaninsu aikin gasa masara na mata ne, amma Basiru bai damu da hakan ba saboda yana so ya cimma mafarkinsa a rayuwa. Bai yarda da cewar wasu ayyuka na tafiya da jinsin mutun ba.

Ga cikakken labarin a kasa:

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng