Aljani kiriku: Messi ya kafa tarihi 3 a cikin wasa daya kacal

Aljani kiriku: Messi ya kafa tarihi 3 a cikin wasa daya kacal

- Dan wasa Messi ya sake kafa tarihi

- Karo na uku kenan Messi na cin kungiyar ta Espanyol

- Dan wasan dai yanzu ya ci wa Barcelona kwallaye 3 a wasa sau 38

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa kungiyar Espanyol da ci 5-0 a gasar La Liga na wasan mako na 3 da suka kara a filin wasan su na Camp Nou.

A karawar ce kuma dai shahararraen dan wasa Lionel Messi ya ci kwallo 3 rigis shi kadai kuma a karo na 38 tun fara yiwa kungiyar ta sa wasa a matsayin kwararren dan kwallo shekaru da dama da suka wuce.

Aljani kiriku: Messi ya kafa tarihi 3 a cikin wasa daya kacal
Aljani kiriku: Messi ya kafa tarihi 3 a cikin wasa daya kacal

KU KARANTA: Mun gama da Boko Haram, saura karasawa

Legit.ng dai ta samu kuma cewa hakan na nufin dan wasan ya kafa tarihi akalla uku bayan wasan da ya ci kwallaye 3 a wasa daya sau 27 a gasar La Liga da kuma sau 7 a gasar cin kofin zakarun Turai da sau 3 a Copa del Rey da sau 1 a Spanish Super Cup.

Haka ma dai mun samu cewa a karo na uku kenan Messi dan kasar Argentina na cin kungiyar ta Espanyol kwallaye 3 a wasa daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: