Wata mahaukaciya ta haihu a bakin hanya a Delta (hotuna)
Wata mahaukaciya ta haifi kyakkywan jariri a bakin hanya a jihar Delta.
A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, Sapele Oghenek, wata yar kasuwa da wata mai wajen siyar da magani ne suka karbi haihuwar matar da taimakon wasu dake kusa.
Oghenek ya bayyana cewa yar kasuwar wacce ke siyar da gasasshen ayaba a kan hanya ce ta lura da cewa matar da nakuda sai ta yanke shawarar taimaka mata.
Yar kasuwar ta nemi taimakon wasu mutane a lokacin da ta lura da cewa mahaifar yaki fitowa.
Ya kara da cewa wata ma’aikaciyar asibiti dake da wajen siyar da magani kusa da yankin ta zo don taimakawa yar kasuwar kuma sunyi nasarar karban haihuwar cikin sauki.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dubban matasan Najeriya sun mamaye Abuja don yiwa Buhari da Najeriya addu’a
Karanta cikakken labarin a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng