Ni fa bada kudin sata na fara kasuwanci na ba - Atiku Abubakar

Ni fa bada kudin sata na fara kasuwanci na ba - Atiku Abubakar

- Tsohon shugaban kasa Atiku ya amsa tambayoyin yan Najeriya a shafinsa na Twita

- Atiku ya musanta zargin da ake masa na cewa da kudin haram ya kafa kamfanoninsa

- Tsohon shugaban yace tun kafin ya shiga siyasa ya mallaki kamfanoninsa

Tsohon mataimakain shugaban kasa Atiku Abubakar ya musanta zargin da ake masa na cewa da kudin sata ya kafa kamfanonin sa.

Ya kuma karyata labarin da ke yawo a gari cewa shi ke da kamfanin kera janarata mai suna Mikano International Limited.

Yayi duk wannan bayannan ne a yayinda yake amsa tambayoyin mutane ta shafin sada zumunta na Tuwita a ranar Alhamis.

Ni fa bada kudin sata na fara kasuwanci na ba - Atiku Abubakar
Ni fa bada kudin sata na fara kasuwanci na ba - Atiku Abubakar

Wani mai amfani da twita mai suna @izz_korede yayi wa Atiku tambaya kamar haka: ''Bayan naji ance kai ke da kamfanin janarata na Mikano, sai jiki na yayi la'asar domin hakan na nufin idan ka zama shugaban kasa, duhu duk zai malale Najeriya.'' (Ma'ana domin kamfanin ka tayi cinikin janareta)

KU KARANTA: Jihohi 10 da sukayi zarra wajen ilimin boko a Najeriya, Duba ko jihar ka ta sami shiga

Atiku ya amsa masa da cewa: ''Abokina, wannan labari ba gaskiya bane amma duk da haka ka fade ta. Na mallaki kamfanoni wadanda sukafi wannan girma da bunkasa, mene zai hana in musanta idan nawa ne?.

Wani mai suna@adewoleade ya sake jefa masa tambaya kamar haka: "Kamfanonin ka ma duk ai da kudin haram ka kafa wanda ka sata daga shekarar 1999 - 2007"

Atiku ya amsa masa da lisafo sunayen kamfanonin da ya mallaka da kuma shekarun da aka kafa su.

1. NICOTES (wanda yanzu ake kira Intels) an kafa shi ne a 1989

2. Prodeco wadda aka kafa a 1996

3. Gona ta 1982

4. Makarantar ABTI kuma an kafa a 1992

Duk da haka wani mai amfani da shafin twita mai suna @ola2all ya rubuta cewa: ''Ai duk kamfanonin basu tabuka wani abin azo a a gani har sai bayan da ka zama mataimakin shugaban kasa, marsa wayyo ne kawai zasu yarda da dabarun ka.''

Atiku ya mayar masa da martani kamar haka: ''Kamfanin intel riga ya shahara a Najeriya wajen harkan man fetur da gas tun kafin 1994. Shiyasa gwamnatin soji sukayi kokarin kwace kamfanin.''

Akwai jita-jitan cewa Atiku zai fito takaran shugabancin kasa a shekarar 2019 amma har yanzu bai bayyana hakan ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164