Kalli Musa, makawo dake sana’ar gyaran takalmi (hotuna)
Anga wani makaho mai suna Musa a jiharJigawa yana aikin karfi yanda ko wani mai kwarjini zaiyi.
Mutumin wanda aka haifa a karamar hukumar Maikyari Kaugama a jihar na aiki a matsayin mai gyaran takalmi.
A wata zantawa da aka yi da wasu mazaunan Abuja, Musa yana aiki ne domin biya wa iyalen sa bukatun su.
Al’amarin Musa dai ya zama abun koyi ga yawancin mutane; yana aiki da kwazo yanda duk wani dan adam mai cikakken gabbai yake iyayi. Ya bayyana kanshi a matsayin mai gyaran takalmi.
KU KARANTA KUMA: Ministoci sun shiga alhini kan goyon bayan Atiku da Aisha Allhassan tayi
Wannan lamarin abun mamaki ne ga kowa, idan har zai tashi daga bacci a ko wace safiya ya tafi wajen aiki, me zai hanani yin aiki irin yanda yake yi?
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng