Abin al’ajabi: Karanta laifin da budurwa tayi ma Saurayinta da har ya caka mata kwalba
- Budurwa ta shiga halin ni yasu bayan yayi saurayinta ya daba mata kwalba
- Saurayin ya shiga hannun hukuma, sa'annan alkali ya dage sauraron karar
Wani matashi ya shiga hannun hukuma bayan ya daba ma budurwarsa Kehinde Olomola kwalba a jihar Legas sakamakon rashin girka masa abinci da matar ke yi masa.
An gurfanar da mutumin ne a gaban kotun majitsir dake karkashin jagorancin Alkali Jimoh Adefioye a ranar alhamis 7 ga watan Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.
KU KARANTA: Wasu matakai guda 10 da Buhari ya ɗaukar ma kansa tun bayan ɗarewarsa karagar mulki
Dansanda mai kara, Sufeta Akpan Ikem ya bayyana ma kotu cewar saurayin mai suna Babatunde Adeoye ya tafka ma budurwar tasa aika aikan ne a ranar 1 ga watan Agusta a rukunin gidaje na Obada, dake Unguwar Badagry.
“Wanda ake zargin ya caccaka ma budurwarsa wuka ne bayan da suka fara musu sakamakon rashin girki da budurwar tayi, hakan ya sanya saurayin caka ma budurwar wuka a kafa da hannayen ta.” Inji Dansandan.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan laifi da mutumin ya aikata yaci karo da sashi na 171 na kundin laifukan jihar Legas, kuma zai iya fuskantar hukuncin shekaru 3 a gidan yari.
Bayan sauraron karar, sai alkali ya dage shari’a zuwa ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2017.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng