Miji da mata sun mutu sakamakon hayaƙin Janareta a Edo (Bidiyo)
Wani mutum Imafidon Ototie tare da matarsa sun rasa rayukansu a ranar Litinin sanadiyyar hayakin janareta daya turnuke su a dakinsu dake karamar hukumar Ikpoba –Okha na jihar Edo.
Hayakin janaretan ya taso ne yayin da aka ajiye janaretan a farfajiyar dakinma’auratan, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Tonon silili: Asirin wata Sanatan Najeriya data sayi gidan naira miliyan 540 a Landan ya tonu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yaron mamatan, mai suna Bright ne ya gano gawar iyayen nasa ne a safiyar ranar Litinin daya dawo, dayake ba’a gida ya kwana ba.
Ganin gawar tasu keda wuya, yasa yaron ya tsala ihu, tana neman taimakon makwabtansu domin su kawo masa agaji, yana kuka yana raki.
Ga bidiyon nan:
Yaron yace ya gargadi iyayen nasa dasu dinga kashe janaretan a kullum idan dare tayi yayin da zasu kwanta barci. “Ji nayi kamar wahayi aka yi min, akan na baro inda naked a sassafen nan, ina zuwa na tsinci gawar iyayena.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng