Biyfara : An kashe dan Najeriya a India akan musun yanci Biyafara
- Wasu sunce hatsarin babur ne yayi sanadiyar mutuwar Chigozie
- Jayayyya akan siyasar Najeriya ya janyo aka masa dukan tsiya
- Yansanda sunce hatsari yayai amma dan uwansa yace kashe aka yi
An kashe wani dan Najeriya mai suna N.Chigozie, a India akan musun neman yancin Biyafara.
An ga gawar mamacin ne a safiyar Litinin a Unguwan Hennur dake Arewacin Bengaluru, wasu sun ce faduwar da yayi akan babur din sa yayi sanadiyar mutuwar sa amma dan uwansa Nonso yace kashe shi aka yi.
A ranar Lahadi ne, Chigozie, Nonso tare da abokan su hudu suka je shakatawa a wani gidan sayar da abincin Africa dake Byrathi, daganan sai suka fara jayayya akan abincin.
“Su shida suka yi rikici akan raba abinci kuma suka ci mutunci juna.Neishko (Nonso) ya tafi asibitin dake kusa da wajen dan duba kan sa sai Chigozie ya bishi akan babur. A lokacin da yake dawowa ne daga asibitin, Chigozie ya mutu,” inji yansanda.
KU KARANTA : Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas
“Ya mutu ne ta sanadiyar hatsari. Binciken farko da aka yi ya nuna Chigozie yana tafiya a hankali akan babur dinsa, kafin yayi hatsari akan titin jirgin kasa kuma ya samu mumunar rauni a kan sa kafi ya mutu. Amma kaninsa Nieskho yace kashe shi aka yi.”
Jaridar Bangalore Mirror, ta rawaito, cewa "an kashe Chigozie ne saboda jayayyan da yayi da abokan sa akan Biyafara.”
“Marigayin da kaninsa sun je shakatawa da abokan su a wani gida dake Byrathi. Daganan sai suka fara jayayya akan siyasar Najeriya. Yansanda suce su biyun aka ma dukan tsiya,”.
“Nonso ya kai kansa asibiti a motar sa bayan dukan da aka mu su .Shi kuma Chigozie an ga gawar sa ne akan titin jirgin kasa bayan ya bar wajen akan babur dinsa.
Nonso yayi zargi kashe dan uwan sa aka yi. Amma bincike ya nuna hatsari ne yayi sanadiyar mutuwar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng