Tsohon dan wasan Hausa, Kasimu Yero ya riga mu gidan gaskiya
Tsohon shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa, Alhaji Kasimu Yero ya cika a yau Lahadi, 3 ga watan Satumba, 2017 bayan doguwar rashin lafiya da yayi
Marigayin ya rasu ne a jihar Kaduna bisa ga labarin da jaridar Legit.ng ta samu.
Shahrarren dan wasan ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen tashan NTA - a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci, Karanbana da sauran su.
KU KARANTA: Gwamnati ta rage kudin mai a Najeriya
Jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya mika sakon ta’aziyyarsa a shafin sada zumuntarsa Instagram inda yayi fatan Allah a jikan marigayin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng