Da dumi-dumi: Mumunar hadarin mota ya faru a hanyar Kaduna zuwa Abuja (hotuna)
Wani mumunar hadarin mota ya faru a babban titin Kaduna zuwa Abuja a yau Lahadi, 3 ga watan Satumba 2017 inda mutane suka jikkata da har da kananan yara
Da ikon Allah, jami’an FRSC sun isa wurin da wuri inda suka kai wadanda suka jikkata asibiti.
Wannan mumunar hadari ya faru ne a karamar hukumar Tafa da ke jihar Neja inda mota kirar Volkswagen saloon tayi rugu-rugu.
Kwanakin nan ne jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa akalla mutane 3 ne suka hallaka a garin Ijebu-Igbo, jihar Ogun a ranan Sallah yayinda wata mota ta ratsa cikin masallata a filin Idi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng