Murnar sallah: Fayose ya saka tufafi da rawani kamar musulmi zuwa sallar idi
- Gwamnan jihar Ekiti kuma kirista ya saka tufafi da rawani kamar musulmi zuwa sallar idi tare da sauran al’ummar musulmi a jihar
- Fayose ya samu kyakyawar tarbo daga shugabannin addinin da sauran al’ummar musulmi
- Gwamnan ya shawarci malamai na Islama cewa su kasance masu gaya wa shugabannin gaskiya
Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose, a ranar juma'a, 1 ga watan Satumba ya saka tufafi da rawani a matsayi musulmi kuma ya shiga yin sallah Eid-Kabir tare da musulmai a Ado Ekiti babban birnin jihar.
Legit.ng ta ruwaito cewa Fayose ya samu kyakyawar tarbo daga shugabannin addinin da sauran al’ummar musulmi a filin sallar idi.
Fayose yayin da yake magana da jama’an musulmai ya ce wannan ba shine karo na farko da ya kasance da al’ummar musulmai ba, ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da dangantakar.
Yace ana bukata irin wadannan ayyuka daga shugabannin ta hanyar yin wa'azin zaman lafiya da kuma hadin kai al’umma.
KU KARANTA: Babban Sallah: Allah yayi wa Najeriya albarka – Sarkin Kano
Fayose ya kuma yi alkawarin yin la'akari da bukatar al’ummar musulmai a jihar.
Ya shawarci malamai na Islama cewa su kasance masu gaya wa shugabannin gaskiya kuma suyi wa'azi game da dabi'un adalci da daidaituwa.
Tun farko, babban limamin na Ado Ekiti kuma shugaban limamai a kudu maso yammacin kasar da jihohin Edo da Delta, Alhaji Jamiu Kewulere-Bello, ya yaba wa gwamnan a cikin jawabinsa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng