Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

-Jami'iyyar PDP tana son tsaya da Attajiri Aliko Dangote a matsayin dan tarar ta na shugabancin kasa a zaben 2019

-Jami'iyyar ta aike da tawaga domin zawarcin attajirin dan kasuwan

-Jami'iyyar PDP tana sa ran Dangote yayi takarar shugaban kasa a karkashin tutar jami'iyyar

Bisa ga dukkan alamu, jami'iyyar PDP tana niyyar tsayar da babban attajirin dan kasuwan nan da yafi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Rahoton jaridar Daily Times yace PDP tana shirye-shiryen zawarcin attajirin dan kasuwan domin yayi takara a jami'iyyar.

Legit.ng ta tattaro cewa jami'iyyar zata tsaida dan Arewa ne a matsayin dan takarar shugaban kasa sannan shugabancin jami'iyyar zata koma sashin kudu.

Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

Wata majiya a jami'iyyar PDP tace ziyarar da jami'iyyar aka kai ma Alhaji Aliko dangote bazai rasa nasaba ta yi masa tayin tsaya wa takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar.

Majiyar tace tuni an ma riga an aike tawagar da zata je zawarcin Aliko Danote, an yanke shawaran hakan ne bayan kwamitin jami'iyyar wanda ta hada da tsohon shugaba Goodluck Jonathan sun tattauna kuma suka yarda cewa shine ya dace yayi musu takara.

DUBA WANNAN: Ya zama dole ni da sauran masu rike da mulki mu tuba - Dino Melaye

"Ina tabbatar maka da cewa jami'iyyar PDP tana zawarcin Alhaji Aliko Dangote domin ya zo yayi takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jami'iyyar a zaben shekara 2019.''

"Anyi la'akari da abubuwa masu yawa kafin shawarar a neme shi. Alhaji Dangote mutum ne mai mutunci da kima a idon jama'a, kuma yayi suna a duk fadin duniya kuma har ila yau yana da kudin da zai iya daukan nauyin duk wani abu da ka iya tasowa wajen fafutukar yakin neman zabe. Mun tabbata zai iya tunkarar duk wani wanda jami'iyyar APC zata tsayar," a cewar majiyan.

Hakazalika, bincike da jaridar Daily Times tayi ya nuna cewa attajirin ya bada gudunmawa wajen yakin neman zaben wasu shugabanin kasar Najeriya.

Wani mamba na kwamitin rikon kwarya na Ahmed Makarfi yace sai nan gaba zasuyi tsokaci akan maganar.

Daga karshe, wani na hannun daman Aliko Dangote da ya nemi a sakaya sunan sa yace Dangote bashi da ra'ayin takarar siyasa, shi yafi son ya cigaba da saka hannun jari a kamfanoni da kuma samar wa da jama'a aikin yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164