Taba Nnamdi Kanu babban kuskure ne - Abubakar Dangiwa Umar
-Kanal dangiwa Umar tsohon gwamnan jihar Kaduna ne a lokacin mulkin soja
-Kama Nnamdi Kanu zai iya janyo tashin hankali
-Yan kabilan Ibo da dama sun kudurta a zuciyan su gwamantn tarayya bata tare da su
Tsohon gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin soji, Kanal Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya, ya ba gwamnati shawara game da kara kama shugaban kungiyan yan asalin Biyafara, Nnamdi Kanu, da magoya bayan sa, da cewa babban kuskure ne a rika daukan su a matsayin yan ta’adda.
Umar yayi wannan gargadin ne a ranar Laraba a wata sanarwa da yayi way an jarida.
Ya ba gwamnati shawara da wata baitin Shehu Usman Danfodio da yace “Hanya mafi sauri wajen rusa daula shine fifita wata kabila aka wata kabila, ko kuma nunu babancin akan al’umma, da kuma janyo wadanda bai kamata a janyo su kusa ba, da kuma korar wadanda ya kamata a janyo kusa.
Umar yakara da cewa yunkurin sake kama Nnamdi Kanu zai janyo tashin hankali, kuma a siyasanci bai da ce ba, saboda shugaban IPOB ba dan ta’ada bane saboda haka a daina mishi kalon dan ta’ada.
KU KARANTA : Ma'aikatan asibiti na zanga-zanga a jihar Ondo ta kai sun hana kowa shiga asibitin
Umar, wanda shine shugaban kungiyan Hadin kai da cigaban kasa, (MUP), yace rahotanni sun nuna gwamnatin tarayya ta umarci kotu ta jnaye belin da aka Nnamdi Kanu saboda aka kara kama shi.
“Wannan yunkurin zai haifar da tashin hankali kuma a akwai gaza wa a siyasance. Nnamdi Kanu ba karamin mutum bane. Matashi ne da yake fafituka neman yanci Kabilan Ibo.
“Yana fada da gwamnatin tarayya ta dalilin hana ba da belin shi da gwamnati tayi.
Nnamdi Kanu da sauran yan Kabilan Ibo sun kudurta a zuciyan su cewa gwamnatin tarayya bata tare da su musamman wadanda suka bashi shugabankasakashe biyar na Kuri’o a lokacin zabe.
“Kafin dimokradiyyar mu ta iya biya bukatan al’ummar ta sai ta koyi hakuri da iya jan kowa a jiki.”
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng