Dubun wani babban fasto mai tsafi da kananan yara ta cika (Hotuna)
- Hukumar 'yan sandan jihar Cross Ribas ta kama wani fasto mai tsafi da yara
- An kama faston tare da wasu mutane 6 a cocinsu
- Hukumar ta ce ta sami wasu abubuwa masu haɗari daga faston da sauran mutane 6
Hukumar 'yan sandan jihar Cross Ribas a ranar Talata, 29 ga watan Agusta ta gabatar da wani babban fasto da ake zargi a jihar. Faston wanda aka gabatar tare da wasu mutane 6 a kan zargin kashe wani jariri mai shekara daya da kuma wata shida da haihuwa wanda ake zarginsa yana amfani da su don yin tsafi.
Kamar yadda Legit.ng ta ke da labari Obo-Ekpenyog shi ne faston coci na Royal God’s Commandment Ministry wanda take Calabar babban birnin jihar Ribas.
A lokacin da aka gabatar wadanda ake zargin, mai magana da yawun hukumar, ASP Irene Ugbo, ya ce an kama mutumin ne da wasu mutane 6 a ranar 24 ga watan Agusta.
Irene ta ce an kama su ne lokacin da iyayen marigayin suka koka cewa wasu ‘yan bindiga wadanda suka rufe fuskansu sun sace 'ya'yansu a gidansu.
KU KARANTA: Yadda wata Malamar asibiti ta kashe marasa lafiya kusan 100
Ta ce nan da nan hukumar ta tura wasu jami’an ‘yan sanda don su bincike cocin da kuma kewaye, kuma sun sami wasu abubuwa masu tsokanar da aka kama da fasto da sauran mutane shida.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng