Dan Najeriya ya ƙirƙiri wata na’aura mai binciko bama bamai

Dan Najeriya ya ƙirƙiri wata na’aura mai binciko bama bamai

- Wani dan Najeriya ya kera wata na'urar kwamfuta mai kwakwalwa

- Wannan na'ura na iya gano bamabamai

An samu wani matashi dan Najeriya mai suna Oshiorenya Agabi ya kera wata na’urar kwamfuta wanda zata iya shishinar bom a duk inda yake, ko aka boye shi.

Mista Agabi ya samu nasarar kera wannan na’aura ne mai suna Koniku ne tare da taimakon kwararru a fanonin ilimi daban daban, inda kuma ya kaddamar da ita a kasar Tanzania.

KU KARANTA: Kwana 1000 na ɓarawo: An yi caraf da ɓarawon Ragon Sallah mai suna ‘Baletolli’ (Hotuna)

Legit.ng ta ruwaito Agabi yana bayani, inda yake cewa na’urar Koniku itace irinta ta farko da aka taba yi a duniya, wanda take iya shinshinar bom daga nesa, tare da jiyo numfashinsa.

Dan Najeriya ya ƙirƙiri wata na’aura mai binciko bama bamai
Agabi

Agabi yace za’a iya amfani da Koniku don maye gurbin jami’an filin sauka da tashin jiragen sama, don shinshino dukkanin wani nau’in bom da aka boye koda a cikin jaka ne.

Dan Najeriya ya ƙirƙiri wata na’aura mai binciko bama bamai
Agabi a bakin aiki

Sai dai masana ilimin kimiyya sun ce babban kalubalen da wannan na’ura zata ci karo da shi, shine wajen siyarwa, inda suke ce babban aiki ne a samu kamfanoni su sayi wannan na’ura.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng