An ceto kanana 'yan matan da aka jefa sana'ar karuwanci a jihar Ogun
-Gwamnatin jihar Ogun ta dade tana wayar da kan matasa kan ilar karuwanci
-Wasu yan mata guda 2 yan kasa da shekaru 20 da suka dade suna sana'ar sunce sun tuba
-Kwamishinan matasa da wasani, Mr Afuape yace gwamnatin jihar zata samar ma yan matan kulawa da kuma sana'a
Bayan kiraye-kirayen da gwamnatin jihar Ogun ta dade tana yi wajen fahimtar da yan mata kan ilar karuwanci, wasu yan mata gida biyu da suka ce suna sana'an sun tuba, kuma sunyi alkawarin baza su sake komawa ba.
A lokacin da yake hira da manema labarai a birnin Abeokuta, kwamishinan wasani ya matasa na jihar, Mr Ofolabi Afuape yace yan matan biyu duk yan kasa da shekaru 20 ne.
Yace wannan nasarar ta biyo bayan gangami da wayar da kai ne da gwamnatin jihar takeyi akan fahimtar da jama'a ilar 'sana'ar'
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dage zartar da hukunci akan gagarimin mai garkuwa da mutane Evans
Afuape yace yan kwamitin sa zasu zaunasu duba irin sana'ar da zai dace da yan matan domin su samu abin dogaro da kai.
Kwamishinan yayi kira da jama'a, iyaye, coci-coci da masallatai su taimaka wajen wayar da kan matasa akan ilolin da ke tatare da muguwar sana'ar a duk lunguna da sakon da ke jihar.
Ya kara da cewa za'a baiwa yan matan kulawa ta musamman, har ila yau, yayi tir da mazajen da ke kula yaran kuma yayi musu nasiha da su dena.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng