Bincike: Rudewa da kasalar kwakwalwa na damun 'yan Nigeria mutum miliyan 7

Bincike: Rudewa da kasalar kwakwalwa na damun 'yan Nigeria mutum miliyan 7

- 'Yan Najeriya a kalla miliyan 7 na fama da gajiya da rudewar kwakwalwa

- Dalilai masu yawa na haifar da ciwon kwakwalwa

- Motsa jiki da gujewa shaye-shaye na karin lafiya

Wani kwarraren likita, Dr. Olabode Shabi, a wani jawabinsa da yayi a taron kungiyar 'yan jaridu ta kasa reshen jihar Ekiti, ya bayyana cewar daga cikin mutum miliyan 29 da ke fama da kasala da rudewar kwakwalwa, miliyan 7 'yan Najeriya ne.

Babban likitan ya bayyana cewar mutane na samun raunin kwakwalwa tare da rikicewar ta saboda dalilai masu yawa, amma tushen matsalolin na farawa ne daga wurin aiki.

Bincike: Rudewa da kasalar kwakwalwa na damun 'yan Nigeria mutum miliyan 7
Bincike: Rudewa da kasalar kwakwalwa na damun 'yan Nigeria mutum miliyan 7

Ya kara da cewar, tsarin wurin aiki musamman lokacin farawa da rufe aiki, matsi a wurin aiki, rashin ingattaccen wurin aiki, rashin tabbas a wurin aiki, da kuma tsoron barin aiki, wato "ritaya".

Ragowar abubuwan da kan iya haifar da wadannan tagwayen matsaloli sun hada da burin son cimma wani buri a wurin aiki, rashin alaka mai kyau da shugabannin wurin aiki, da kuma zurfin ciki.

Likitan ya ce "ba wani mahaluki da yake da kariya daga wadannan matsaloli masu addabar kwakwalwa".

Dr shabi ya bayyana alamomin wadannan matsaloli da suka hada da yawan bacin rai, rashin karsashin yin komai, gajiya, yawan mantuwa, rashin samun nutsuwa, kasa tsayar da shawara, daukewar sha'awar abinci, rama, da damuwa.

Dr. Shabi yace 'matsalar na iya samun hatta wadan da basa aiki musamman masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ko shan magunguna ba bisa ka'ida ba.'

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya zata biya ladan kudi N500,000 ga duk wani mai labari a kan 'yan kunar bakin wake

A karshe Dr. Shabi yace, 'ware lokaci domin motsa jiki da yin raha, cin abinci mai lafiya, gujewa shan giya, kwayoyi, da tabar sigari, rage shan sikari da gahawa, bayyana matsala ga makusanci, da kuma samun isashshen barci ne manyan hanyoyin kare kai daga kamuwa daga wadannan matsaloli, yana mai bayyana cewar "Rigakafi dai ya fi magani".

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng