Yawan tafiyan Gwamna Ben Ayade ya sa ma'aikatan gwamnatin jihar sun daina zuwa aiki
-A tarihin Najeriya babu dan Najeriyan da ya kai Ben Ayade yawan tafiye tafiye
-Dole majalisar dokokin jihar sun tsige shi saboda saba kai'dojin tafiya
-Tunda Ayade ya zama gwamna bai taba yin kwana dari a ofishin sa ba
Rashin zaman gwamnan jihar Cross Rivers, Prof Ben Ayade ya durkusar da aikin gwamnati a jihar, saboda ma’aikatan jihar suna barin bakin aikin su, zuwa wajen biyan bukatun su. A binciken da yan jaridar Daily Post suka yi sun gano cewa wasu ma'aikatan kasuwanci suke zuwa yi. Abun da ke faruwa kenan duk lokacin da gwamnan yayi tafiya zuwa Turai.
Yanzu haka, masu aiki karkashin ofishin gwamnan sun bar bakin aikin su, zuwa wajen kasuwancin su. Ofishin gwamna ya zama Kaman makabarta inda babu kowa.
Legit.ng ta samu rahoton cewa babu gwamnan da yakai Ben Ayade yawan tafiye-tafiye.Kuma duk lokacin da yayi tafiya sai tattalin arzikin jihar ta samu matsala.
Kungiyan CTRNI ta yi kira da majalissar dokokin jihar cross Rivers da su fara yunkurin tsige gwamnan jihar Ben Ayade saboda yawan tafiya tafiyen da sa, wanda ya saba ka’ida.
KU KARANTA:'Yan Majalisar Kasar Amurka sun gana da Bukola Saraki
A wani taro da kungiyan tayi a Calaba ta ce tun da Ayade ya zama gwamnan jihar yafara tafiye tafiyen banza. A tarihin Najeriya ba a taba samun gwamnan da yakai shi yawan tafiya ba.
Mai kula da harkokin kungiyan , Kwamared Jonathan Agbor, yace ya zama dole majalissar dokokin jihar su tsige Ayade dan saba dokar tafiya, saboda ya mika wa mataimakin sa mulki duk lokacin da zai yi tafiya haka yake barin jihar ba jagora. Da kuma barnatar da kudaden jihar saboda yawan tafiyar sa
Agbor yace “Tunda Ayade ya hau mulki, kwanakin da yayi a Abuja da kasashen waje yafi kwanakin da yayi a jihar sa yawa, yakara da cewa a cikin ranaku 365 da ake da shi a shekara Ben Ayade bata yi kwana dari a ofishin sa ba”.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng