Jerin dukiyoyin da tsohuwar ministan mai, Diezani Alison-Madueke, ta handama
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta zage dantse wajen yakan wadanda suka jiwa tattalin arzikin Najeriya rauni
Bayan garkame tsohon NSA, Sambo Dasuki, wanda ya handami kudin makamai $2bn, tsohuwar ministan man fetur, Diezani Alison Madueke, tayi mumunar raunata tattalin arzikin Najeriya.
Amma tun kafin shugaba Buhari ya hau mulki ta arce kasar Landan.
Ga jerin kudaden da aka gano zuwa yanzu:
1) Wadanda aka kwace din-din-din
$153Million (kudi a hannu)
Gida kimanin kudi $37.5
$2.7 Million (kudi a hannu)
N84.5 Million (kudi a hannu)
N7.6 Billion (kudi a hannu).
2) Kwacewan wucin gadi
Dukiyan $22 Million (Gidaje 56)
KU KARANTA: Diezani : Charly Boy, Adeyanju, da sauran su suna shirme ne kawai – Fadar Shugaban kasa
3) Wadanda gwamnatin Birtaniya ta kwace:
£9.8Million
4) Wanda EFCC ke shirin daskararwa:
$20.15M Dukiya a Dubai.
Jimilla:
$155.7Million (kudi a hannu)
$79.65 Million (dukiyoyi)
£9.8 Million (dukiyoyi)
N7.684.5Billion (kudi a hannu)
Jimilla a kudin Najeriya - N94.8Billion
** Farashin canjin da akayi amfani da shi
$ - N350
£ - N460
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng