Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon Sanata Kanti Bello rasuwa
Tsohon sanata daga jihar Katsina, Arewacin Najeriya, Kanti Bello, ya rasu.
Bello, wanda ya wakilci yankin Daura tsakanin shekarar 2003 da 2011, ya rasu ne a safiyar ranar Talata, 29 ga watan Agusta, 2017 a Abuja.
Tsohon shugaban rinjaye na majalisar dattawan ya rasu sakamakon wani rashi lafiya da ba’a tabbatar ba tukuna.
Legit.ng ta samu labarin cewa Kabir Faskari, kanin tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina, Abdullahi Faskari, ne ya tabbatar da mutuwarsa a wata sanarwa.
KU KARANTA KUMA: Ya kamata mata su dogara da kansu ba wai a kan mazajensu ba – Jaruma Fati Bararoji
“An umurci na sanar da kowa cewa munyi rashi na Sanata Kanti Bello a safiyar yau (Talata) a Abuja. Zaá sanar da yadda jana’iza zata kasance anjima.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng