Ko za a je Sallar Jumu'a idan sallar idi ta fado a Ranar ta Juma'a?

Ko za a je Sallar Jumu'a idan sallar idi ta fado a Ranar ta Juma'a?

- Mun tattaro maganar Malamai game da faduwar idi a ranar Juma'a

- Wasu na ganin idan hakan ta faru babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a

- Har wasu manyan Malaman ma na ganin cewa Sallar Azahar ta fadi

A daidai lokacin da ake shirin bikin babban idi mun tattaro maganar Malamai game da faduwar idi a ranar Juma'a kamar yadda za ta kama wannan karo daga wani darasi na babban Malamin musulunci Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu.

Ko za a je Sallar Jumu'a idan sallar idi ta fado a Ranar ta Juma'a?
Jama'a wajen Sallar idi kwanaki

1. Magana ta farko

Malaman Malikiyyah sun tafi a kan cewa dole ne ayi sallar Juma'a ko da ta fadi a ranar idi don haka Allah Madaukaki yayi umarni a Qurani asali.

KU KARANTA: Tofa: Ana shirin tona asirin Shekau

2. Magana ta biyu

Malaman Shafiiyah na ganin idan hakan ta faru babu wajibcin zuwa Sallar Juma'a ga wadanda su ka fito daga kauyukan nesa amma mutanen gari za su yi Juma'a.

3. Magana ta uku

Akwai 'yan mazhabar Hanabila da su ka tafi akan cewa idan hakan ta faru to sallar idi ta dauke Sallar Juma'a gaba daya.

4. Magana ta hudu

Akwai Malamai irin su Imam Shawkani da ke ganin idan Idi ya fado a Juma'a to har sallar Azahar ta fadi amma wannan magana na sa akwai rauni.

Magana mafi inganci inji manyan Malamai ita ce za a yi sallar idi sannan kuma mustahabbi ne Liman yayi sallar Juma'a ga masu niyya amma ba dole bane don kuwa wata idin ta dauke wata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya na farin cikin dawowar Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng