Atiku Abubakar ya yabawa Shugaban kasa Buhari

Atiku Abubakar ya yabawa Shugaban kasa Buhari

- Alhaji Atiku Abubakar ya yaba da kokarin Shugaba Buhari

- Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya soki maganar raba kasar

- Shugaba Buhari ya kama hanyar maganin masu wannan kira

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar nan Alhaji Atiku Abubakar ya jinjinawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Atiku Abubakar ya yabawa Shugaban kasa Buhari
Atiku Abubakar tare da Shugaban kasa Buhari

A halin yanzu wasu na kira a raba kasar musamman wasu 'Yan Kungiyar ACYF ta Matasan Arewa da kuma Kungiyar IPOB ta 'Yan Biyafara wanda Shugaban kasar yayi kira da Jami'an tsaro su yi maganin masu wannan yunkuri yace babu maganar raba Najeriya.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya sauya Ministoci - NLC

Atiku Abubakar ya yabawa Shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Buhari da Atiku Abubakar

Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya yabawa Shugaban kasar a dalilin wannan kira da yayi. Atiku Abubakar ko da yana goyon bayan ayi wa Najeriya garambawul bai yarda a raba kasar. Atiku ya kuma yi kira ga Dattawan kasar su yi kokari wajen ganin an hada kai a Najeriya.

Shugaban kasa Buhari ya zauna da Shugabannin Jam'iyyar PDP da APC bayan nan kuma ya kuma gana da kaf Gwamnonin kasar a karshen makon dalilin wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Beraye sun fatattaki Buhari daga Ofis

Asali: Legit.ng

Online view pixel