Yadda noman cita ke inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna

Yadda noman cita ke inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna

-Cita yana inganta lafiyar jikin dan Adam

-Ana sayar da Buhu cita 25,000

-Bana bukatan aikin gwamnati saboda noman cita yana biya mun dukan bukatu na

Cita daga kananan hukumomin jihar Kaduna wadanda suka hada da kagarko, Jaba da Kachia wanda sune garruruwan da aka fi sani da noman cita a Najeriya, kuma bincike ya nuna cewa citan su yafi kowani cita kyau a duniya.

Ana noman cita dayawa a Nok, Tsakiya da Kwoi a Jaba, Walijo, Maraban Walijo da Gidan Mana a karamar Hukumar Kachia da Kubacha, Aribi da Katugal a karamar Hukumar Kagarko, duk a Jihar Kaduna.

Ginger yana daya daga cikin kayan dandano da ake amfani da shi a cikin abincin zamani.

Cita yana da amfani sosai wajen inganta lafiyar jiki, yana magance matsalar ciwon zuciya,ciwon ulsa, ciwon sukari, kitsen jiki, ciwon daji, radadin jiki, shanyewan jiki, da matsalar rashin narkewan abinci, wata kila wannan shine dalilin da yasa mutane dayawa suka fara noma da sayar da cita.

Yadda noman cita ke inganta ruywar al’ummar jihar Kaduna
Yadda noman cita ke inganta ruywar al’ummar jihar Kaduna

Yadda noman cita ke inganta ruywar al’ummar jihar Kaduna
Yadda noman cita ke inganta ruywar al’ummar jihar Kaduna

Wani manomi mai suna Alhjaji Sulieman Jamo Kagarko, a lokacin da yake zanta wa da yan jaridan Daily Trust, ya bayyana cewa, yakai shekaru 20 yana noman cita, kuma idan gwamnati ta sa hanun jari a harkar, za tasamu Kudaden shiga. Saboda ana sayar da buhu daya na cita N25,000.

KU KARANTA:A karshen wannan makon ne kungiyan malaman jami’a zasu yanke shawara game da yajin aiki

"A kowani shekara masu bukatan cita suna karuwa, kuma yanzu manoman cita sunyi yawa amma matsalar da ake fuskanta shine na taki ne da maganin kwari,” inji shi.

Ya ce kasuwan cita tana karayin albarka sabdoa mutane daga kasashen waje suna zuwa Najeriya sayan citan mu. Saboda citan Najeriya yafi kyau a duniya.

Wani matashi mai suna Dangana Habu daga kurmin musa a karamar hukumar Kachia ya fa da yan jarida cewa, iyayen sa manoma cita ne.

Ya ba da labarin cewa “Iyayen mu a baya suna noman cita ne dan amfanin kan su, saboda a lokacin babu masu sayan cita, dan mutane dama a lokacin basu san amfanin cita a jikin dan Adam ba.

Amma yanzu manoma cita dayawa suna jin dadin rayuwar su . Daga noman cita na siya motar da nake hawa da gidan da nake zama a ciki, da shi kuma nake kula da iyali na. Bani da lokacin yin aikin gwamnati saboda aikin noma yana biya mun duka bukatu na.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: