Kiwon lafiya: Bayani game da cutar HPV 'Papiloma'
- Cutar Papilloma na kashe Jama'a cikin ruwan sanyi
- Babu cutar da ke kisa irin wannan mugun ciwo
- Ana daukar cutar nan ne wajen kwanciyar aure
Cutar Papilloma na cigaba da kashe Jama'a da dama musamman a wanna yanki na kasar nan da ma Duniya gaba daya.
Bincike ya nuna cewa babu irin cutar da ke mugun illa wajen kashe garkuwar haihuwa kamar cutar HPV watau Human Papilloma Virus. Ana daukar cutar ne wajen zaman aure amma ba dole sai wajen kwanciya ba. Akwai dai nau'o'in cutar iri-iri.
KU KARANTA: Matasa sun kona wani coci a Najeriya
Wannan cutar kan lalata hannuwa da kafafu da sauran sashen jikin mutum. Cutar kan addabi masu aure ne da zarar kwayar ta shiga jikin mutum. A kan dauki cutar lokacin da aka taba mai cutar. A hankali dai cutar za ta ci mutum fatar jikin sa tayi ta barkewa har abin ya munana.
Shekaru 3 da su ka wuce cutar Ebola ta hallaka mutane kusan 50 a annobar da ta barke a Afrika. Gaba daya dai a shekarar 2013 annobar tayi barna a Afrika musamman irin su kasar Liberia, Guinea, da Sierra Leone inda aka rasa mutane sama da 11,000.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Beraye sun tasa Shugaban Najeriya a gaba
Asali: Legit.ng