Wasu yan kasa nagari za su fara gangamin ganin Buhari ya dawo da Diezani Najeriya a hukunta ta
Wasu gungun yan kasa na gari da kungiyoyin sa kai sun sha alwashin fara wani zaman dirshan na kwana biyu domin su tursasawa gwamnatin tarayya da a halin yanzu ke a hannun shugaba Buhari domin ya gaggauta maido da tsohuwar ministar mai Diezani Allison-Madueke gida ta kuma fuskanci shari'a.
Labarin da muka samu dai yanzu shine zaban dirshan din dai za'a yi shi ne a gaban babbar Hedikwatar hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice dake a unguwar Wuse, Abuja.
Legit.ng ta samu dai cewa tsohuwar ministar albarkatun man fetur din a zamanin mulkin shugaba Jonathan yanzu haka dai tana a kasar ta Ingila inda kuma ake zargin ta da tara dukiya mai tarin yawa ba ta halastacciyar hanya ba.
Duk da dai cewa da yawa daga cikin dukiyoyi da kaddarorin da ta mallaka ya zuwa yanzu kotuna sun mallakawa gwamnatin tarayya amma dai har yanzu ba ta gurfana ba gaban kotun.
Asali: Legit.ng