Gusau: Gwamnatin Zamfara za ta gina hanyar Gusau zuwa Birnin Gwari

Gusau: Gwamnatin Zamfara za ta gina hanyar Gusau zuwa Birnin Gwari

- Gwamnatin jihar Zamfara za ta gina hanyar Gusau zuwa Birnin Gwari wanda za ta hada jihar da wasu jihohi 3

- Kamfanin Zhonghao ne zai gudanar da aikin gina hanyar

- Hanyar za ta hada Zamfara da jihohi uku, Kaduna da Kebbi da kuma Neja

Gwamnatin jihar Zamfara ta nuna aniyarta ta fara sake gina hanyar Gusau zuwa Birnin Gwari mai kilomita 132.7 wanda ke kan iyaka da jihar Kaduna ta hanyar Dansadau.

Mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala, ya bayyana wannan a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta a Gusau a karshen wani taron kwamitin kudi da ayyuka tare da kamfanin gine-ginen da za ta gudanar da aikin.

Kamfanin da ake sa ran za ta gudanar da aikin ita ne Zhonghao.

Gusau: Gwamnatin Zamfara za ta gina hanyar Gusau zuwa Birnin Gwari
Gwamnatin jihar Zamfara, Abdulaziz Yari

Wakkala, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin, (FGPC), ya shaida wa manema labaru cewa za a fara aikin ne bayan da aka sanya hannu a yarjejeniyar nan gaba kadan.

KU KARANTA: Shugaban APGA ya yabi Buhari, yace Allah ne ya aiko shi

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa, aikin gina hanyar zai inganta ayyukan tattalin arziki da aikin gona a yankin.

A cewarsa, wannan zai yi sanadiyar bude wasu kasuwanni da dama, ya kara da cewa hanyar za ta hada Zamfara da jihohi uku, Kaduna da Kebbi da kuma Neja.

Legit.ng ta ruwaito cewa taron ta samu halarcin wakilai na kamfanin Zhonghao.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng