Gasar zakarun turai: Yau za'a raba jadawalin kungiyoyin da zau fafata

Gasar zakarun turai: Yau za'a raba jadawalin kungiyoyin da zau fafata

A yau ranar Alhamis din nan ne dai za'a rarraba jadawalin kunyiyoyin da za su fafata a cikin gasar kwallon kafa ta zakarun turai ta karar wasannin ta 2017/2018 wanda za'a gudanar a garin Monaco.

Kamar kuma dai yadda aka saba, al'adar gasar shine babu kungiyar da za ta kara da wadda take kasa daya a wasannin rukuni, yayin da kuma ko wace shekara mahukunta za su sanar da yadda za a raba kungiyoyin.

Gasar zakarun turai: Yau za'a raba jadawalin kungiyoyin da zau fafata
Gasar zakarun turai: Yau za'a raba jadawalin kungiyoyin da zau fafata

Legit.ng ta samu kuma cewa da zarar an rarraba jadawalin ake sa ran fara buga wasannin a cikin rukunonin tsakanin 12 da kum 13 ga watan Satumbar wannan shekarar yayin da kuma za'a yi wasan karshe a watan Mayun shekarar 2018 a Kyiv.

Haka ma dai kuma a lokacin rarraba jadawalin ne dai za a sanar da gwarzon danwasan da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da babu kamarsa a Turai a shekarar nan da sauran kyaututtuka da dama.

Kungiyar Real Madrid ce ke rike da kofin Zakarun Turai na 2016/17 na 12 da ta dauka jumulla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel