Dalilai 5 da yasa za mu shiga yajin aiki a jihar Zamfara – Kungiyar Kwadago

Dalilai 5 da yasa za mu shiga yajin aiki a jihar Zamfara – Kungiyar Kwadago

Kungiyar Kwadago wato NLC sashin jihar Zamfara ta bagwamnatin jihar wa’adin kwanaki 21 kan ta biya ma’aikatan jihar hakkokin su ko ta shiga yajin aiki.

Shugaban kungiyar, Bashir Marafa ne ya bayyana hakan bayan an kammala taron gaggawa da suka gudanar tare da kungiyoyin kwadago ta ‘TUC’ a Gusau, babban birnin jihar Jigawa a ranar Litinin.

Bashir Marafa ya bayyana dalilan da ya suka yanke shawarar tafiya yajin aikin kamar haka;

1. Rashin mayar da hankali gurin cika alkawaran da gwamnati ta daukar wa ma’aikatan jihar tun shekaru shida da suka gabata.

2. Har yanzu wasu ma’aikata har yanzu na karban naira 18,000 a matsayin albashi.

Dalilai 5 da yasa za mu shiga yajin aiki a jihar Zamfara – Kungiyar Kwadago
Dalilai 5 da yasa za mu shiga yajin aiki a jihar Zamfara – Kungiyar Kwadago

3. Gwamnatin jihar ta ki kara wa ‘yan fansho kudin fansho wanda ya kamata a yi tun shekaru biyar da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Wa’adin barin gari: Fadar shugaban kasa ta gana da matasan Arewa

4. Rashin daukan ma’aikata musamman yadda wasu suka yi ritaya ko kuma sauya gurin aiki.

5. Rashin biyan albashin ma’aikata 1,400 da ta dauka tun a shekara ta2014.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng