Allah ɗaya gari banban: kalli yadda ýan matan wata ƙabila a ƙasar Habasha ke yin kwalliya
- Ana samun kabilar Suri a kudancin kasar Habasha
- Yan kabilar Suri makiyaya ne sosai da basu da arzikin da ya wuce shanu
Kabilar Suri dake kasar Habasha a yankin Omo tayi fice wajen sanya ma yayansu mata faranti a baki da sunan kayatar da kyawun yan matan, girman bakin budurwa shine, tsadar sadakinta.
Jaridar Daily Mail ayi wani nazari akan wannan kabilar ta Afirka, masu al’adar ban mamaki, inda da zarar mace ta kai munzalin balaga, sai a cire hakoranta na kasa guda biyu, sai a huda wani karamin rami har zuwa lebenta na kasa.
KU KARANTA: Wuyan aiki ba’a fara ba: Wasu Alhazai 9 sun isa Madina akan Keke daga ƙasar Birtaniya
Bayan yin haka ne sai sanya mata dan faranti da aka yi da laka a bakin nata, kadan kadan za’a dinga kara girmansa, da haka girman leben nata zai dinga karuwa. Leben na kara girma, yawan shanun da za’a bayar a matsayin sadakinta na karuwa, inda ake bada shanu 40 zuwa 60.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito su kuma mazan su kanyi irin nasu al’adar gargajiyar, inda suke fenti jikinsu, ana hada fentin ne da magungunan gargajiya da tabo, duk da nufin jan ra’ayin yan matan.
Sai dai kamar duk wasu al’adun gargajiya, an fara samun wasu yan kabilun Suri dake nuna kiyayya ga irin wannan al’ada mai tsananin azabtarwa.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Zaka iya aure daga kabilar da ba taka ba?
Asali: Legit.ng