Labarin yadda ta kasancewa wata mata da take auren maza biyu lokaci guda
Wata mata mai matsakaiciyar shekaru a garin Ibadan dake jihar Oyo, tana neman yardar kotu wajen sakin daya daga cikin mazajenta guda biyu.
Wannan mata Modinat Mufutau, ta bayyana wa kotu a ranar Talatar da ta gabata cewa, ta auri wannan mazajen biyu saboda ta samu isassun kudin daga wajen su da zasu ishe ta wajen kulawa da 'ya'yan ta guda uku.
Modinatu ta na da 'ya'ya biyu da mijin farko (Mufutau) da kuma da daya ga wani mijin (Saheed).
A halin yanzu dai wannan mata tana rokon kotu da ta raba auren ta na shekaru 12 da Ajadi Mufutau domin a cewar ta ba ya kulawa da ita kuma ba ya jinkanta.
Ta shaidawa kotun cewa ta hadu da Mufutau ne a shekarar 2005, kuma ta dauki juna biyu tare da shi ba tare da yin aure ba, wanda a farko tarayyar ta su ya nuna ma ta cewar shi na gari sai da tafiya tayi nisa kuma ya canja fuska.
"Na bar gidan Mufutau bayan na haihu inda na fara tarayya da wani Saheed wanda na samu juna biyun sa bayan shekaru biyu da fara tarayyar ta mu, inda shima anan ya sauya fuska yana zalunta ta."
"Ban yi wata-wata ba shima na gudu na koma gidan tsohon miji na Mufutau kuma aka yi sa'a na samu wani juna biyun na shi amma sai ga Saheed yazo yana roko na domin na dawo gidan sa."
"Na yanke shawarar ci gaba da tarayya da su duka biyu amma sai wata matsala ta barke yayin da suka hadu da juna a wani gidan haya da nake zama inda suka baiwa hammatar su iska."
KU KARANTA: Magudin Jarrabawa: Jami'ar Dustinma ta sallami malaman ta 3 da dalibai 9
Tana rokon kotu, "na yanke shawarar na saki Mufutau saboda ya dakatar da ba ni kudi da zan rinka kulawa da yaran sa biyu".
Shi kuwa Mufutau bai ce komai akan rokon da Modinat take yiwa kotu ba, sai dai yace "ba shi da masaniyar tarayyar ta da Saheed sai da ya hadu da shi a gidan ta na haya kuma wannan abin kunya ne domin ita ba ta ganin wai wannan abu da ta yi abinda bai dace ba ne."
"Ina dai rokon kotu da ta bani damar ci gaba da rikon dan mu na farko domin na ba shi kulawa ta gari kuma na yi alkawarin ci gaba da tallafa ma ta wajen kulawar dan na mu na biyu".
Alkali mai shari'a, Mukaila Balogun ya aminta da duk rokon su kuma ya amsa mu hakan, kuma ya umarci Mofutau da ya rinka biyan Naira 3,500 a kowane wata don tallafawa Modinat wajen kulawa da dan na su na biyu.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng