An kama mutum da kasusuwan mutane, harda hakarkari da kokon kai, ko me yake dasu, duba

An kama mutum da kasusuwan mutane, harda hakarkari da kokon kai, ko me yake dasu, duba

- An kama wani mutum mai suna Shehu Gidado dan shekara 30 da kasusuwan mutane har da hakarkari da kokon kai a tare da shi

- An gurfanar da malam Gidado a gaban kotu a Legas game da kama shi da aka yi da sassan jikin mutane

Malam Gidado mai maganin gargajiya ne da ke da shekaru 30 da haihuwa, kwatsam, sai ya shiga hannu bayan da aka kama shi da kasusuwan mutane ciki har da hakarkari da kokon kai.

An kama mutum da kasusuwan mutane, harda hakarkari da kokon kai, ko me yake dasu, duba
An kama mutum da kasusuwan mutane, harda hakarkari da kokon kai, ko me yake dasu, duba

Mai shari'ar Sunday Fatola, ya shaidawa kotu inda aka kama Malam Gidado. An kama shi akan hanyar Ogbomoso - Ilorin har da wasu hakarkarin mutane a tattare da shi wanda ya sabawa dokar kasa. A kan hanyar ne ‘yan sanda suka tsaida motar da Malam Gidado ke ciki, duba motar da suka yi suka ga sassan jikin kulle a bakar leda.

Malam Gidado ya musa zargin da ake masa, sannan bai bada cikakken bayanin yadda ya samo sassan jikin mutanen ba.

DUBA WANNAN: Beraye sun yi kaka-gida a Ofishin Shugaban Kasa

Chif Majistare, Abdullatif Adebisi ya bada belin Malam Gidado akan N200,000 a gaban shaidu da daga karar zuwa watan Nuwamba.

Ana yawan samun masu son amfani da sassan mutane da sunan wai suna tsafi, basu dai sani ba cewa chami duk shirme ne, babu yadda za'ayi jikin mutum ya zama kudi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel